Za a gudanar da taron dandalin tattaunawa kan yaki da talauci da samun ci gaba tsakanin manyan jami'ai a shekarar 2015 a nan Beijing, inda shugaba Xi Jinping na kasar Sin zai halarta tare da yin jawabi.
Ofishin yada labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ne ya bayyana hakan a yau yayin taron manema labaran da ya shirya.
Mataimakin darektan ofishin yada labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin Guo Weimin ya bayana cewa, bayan babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 18 a shekarar 2012 ya zuwa yanzu, kasar Sin ta samu sabon ci gaba wajen yaki da talauci. A sa'i daya kuma kasar Sin ta gamo wahalhalu da kalubalolin da take fuskanta. Don haka akwai jan aiki a gabanta wajen fitar da dukkan muhimman gundumomin kasar da kuma mutane fiye da miliyan 70 daga talauci kafin shekarar 2020.
Har wa yau mista Guo ya ce, kasar Sin ta samu goyon baya daga kasashen duniya wajen yaki da talauci, baya ga gudummowar da ta bayar a duniya. Ci gaban da kasar Sin ta samu wajen yaki da talauci ya kara azama kan saurin raguwar yawan masu fama da talauci a duk fadin duniya. (Tasallah Yuan)