Shirin na sa ran horas da jami'ai daga kasashen Uganda, Tanzania, Zambia da wasu kasashen Afirka, ta yadda za a kyautata fasahohinsu na aikin gona da kuma yadda za su inganta dabarun adana amfanin gona da yin rigakafin hadarin da abin ya shafa.
Haka kuma, shirin na WFP zai zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsa da kasar Sin, domin gabatar da fasahohin kasar Sin a fannin aikin gona cikin kasashen duniya, ta yadda za a taimaka wajen kawar da matsalar karancin abinci a duniya da kuma ciyar da hadin gwiwar kasashe masu tasowa gaba. Haka kuma, ana sa ran gabatar da irin fasahohin da kasashen duniya suka samu a lokacin wannan horo ga yankunan kasar Sin dake fama da karancin abinci a halin yanzu. (Maryam)