A shekarun baya baya nan, an samu bunkasuwar sha'anin kiwon dabbobi a kasar Sin, ta yadda karfin samar da dabbobin kiwo ya yi matukar karuwa, tare da bunkasar cinikayyar nama da kuma madarar dabbobin. An ce yawan naman shanu da ka samu a shekarar 2014 a kasar Sin, ya kai ton miliyan 6.89, yayin da yawan naman raguna ya kai ton miliyan 4.28, sai kuma yawan madara wanda ya kai lita ton miliyan 37.25. (Zainab)