Kwanan baya, bisa labarin da wakilinmu ya samu daga taron kara wa juna sani kan sakamakon da kamfanin ketare na Syngenta ya samu bayan da ya gudanar da "shirin raya aikin gona mai tsabta" a shekara ta farko, an ce, yanzu, kamfanin Syngenta ya cimma burin kara samun yawan hatsi da rage yin amfani da magungunan kashe kwari ta hanyar amfani da ire-iren shuka masu inganci tare da samar da horo ga manoma kan yadda za su yi amfani da magungunan kashe kwari da sauransu.
Sin ta zama wani muhimmin yanki da ake gudanar da shirin raya aikin gona mai tsabta na kamfanin Sygenta. A shekarar 2014, kamfann ya kafa wuraren shukkan gwaji 34 a Sin kan yadda za a warware matsalar da ake fuskanta wajen shuka masara, shimkafa da dankali da nau'o'in abinci.(Bako)