Bankin duniya ya yi kira a ranar Talata ga nahiyar Afrika da ta kara kason kudaden da take kashewa a fannin noma, ta yadda za ta kara kiyaye tsaron abinci.
Karancin zuba jari ga aikin noma ya sanya bangaren noma a Afrika kasancewa cikin rauni tare da sauye sauyen yanayi, in ji mista Ademola Braimoh, masani a fannin kula da albarkatun halittu na bankin duniya a yayin wani dandalin harkokin kasuwanci a birnin Nairobi.
Wadannan kalubale, ana iyar haye su ta hanyar kara zuba jari a cikin wasu hanyoyi kamar misalin noma bisa kiyaye muhalli, in ji mista Braimoh a yayin bikin kaddamar da rahaton bankin duniya kan kara samar da albarkatun noma, da kuma juriyar noma bisa nagartattun ayyukan noma da yanayi.
Fiye da mutane miliyan 220 yanzu haka suke fuskantar karancin abinci a Afrika, kuma wannan adadi zai iyar karuwa zuwa fiye da miliyan 350 nan da karshen shekarar 2015, sai fa idan an dauki niyyar aiwatar da muhimman matakai domin fuskantar sauyin yanayi da ke karuwa, in ji darektar kasa ta bankin duniya a kasar Kenya, madam Diarietou Gaye. Sauye sauyen yanayi babbar barazana ce ga ci gaba da ya kamata a fuskanta domin yaki da talauci, in ji madam Gaye.
A shekarar 2003, kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta amince da sanarwar Maputo kan tsaron abinci, da ke kiran dukkan kasashen Afrika da su ware a kalla kashi 10 cikin 100 na kasafin kudinsu ga fannin noma. (Maman Ada)