Tawagar kwararrun kasar Sin a fannin aikin gona mai kunshe da mutane 15 ta isa kasar Namibia, domin gudanar da aikin hadin gwiwa na shekaru 2.
Tawagar wadda ta isa Namibia a jiya Laraba, ta samu tarba daga ministan ma'aikatar ayyukan gona, ruwa da gandun daji na kasar John Mutorwa, da kuma jakadan kasar Sin dake kasar Xin Shunkang.
Mambobin tawagar wadda za ta gudanar da ayyukan ta karkashin yarjejeniyar kasashen Kudu maso Kudanci, wadda hukumar abinci da aikin gona ta MDD ko FAO ta assasa, za su gudanar da ayyuka ne tare da jami'an ma'aikatar ayyukan gona ta Namibian a yankuna 4 dake kasar.
A shekarar da ta gabata ne dai Namibia da kasar Sin suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa, wadda za ta bada damar samar da taimakon masana a fannin ciyar da aikin gona gaba a Namibia.
A jawabinsa na maraba da tawagar kwararrun, jakadan kasar Sin a Namibia Xin Shunkang, cewa ya yi, wannan ne karon farko da kasar Sin ke hadin gwiwa da Namibia a fannin noma, kuma kasarsa na fatan hakan zai ba da damar cimma moriyar juna tsakanin sassan biyu. (Saminu)