in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na kokarin janyo hankalin masu zuba jari a fannin noma
2015-09-02 09:59:35 cri

Gwamnatin kasar Najeriya ta cimma wasu manyan ayyuka domin janyo karin masu zuba jari daga kasashen waje a bangaren noma, in ji wani jami'in gwamnatin kasar a ranar Litinin.

Wannan na daga cikin yarjejeniyar da aka cimma a birnin Abuja, hedkwatar Najeriya, tare da ma'aikatar noma da ci gaban karkara ta tarayya, in ji Joel Attah, kakakin hukumar bunkasa zuba jari ta Najeriya.

Kafin bunkasuwar bangaren man fetur, noma ya taba zama babban ginshiken ci gaban tattalin arzikin Najeriya, in ji mista Attah, inda ya kara da cewa, masu zuba jari za su amfana da ayyukan kulawa na wannan hukuma.

Haka kuma, kakakin ya yi kiran ma'aikatar da ta ba da tabbatancin cewa, masu zuba jari da suka rigaya suka shiga wannan bangare, hakika hukumar ta yi rijistan su domin kare jarin da suka zuba.

A cewar wannan jami'i, hukumar ita ce ma'aikatar gwamnati kadai dake hurumin kula da bunkasa da janyo hankalin masu zuba jari a cikin tattalin arzikin Najeriya.

Har ila yau, hukumar ta kasance wani tsarin shari'a na dukkan fannonin dake da nasaba da zuba jari. Wannan hulda za ta samar da ayyukan yi da karin arziki, in ji mista Attah. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China