in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanan Afirka sun yi kira da a koyi da kasar Sin a fannin raya aikin gona
2015-04-10 11:55:17 cri

An bude taron kara wa juna sani game da zuba jari da kasar Sin ke yi a kasashen Afirka a fannin aikin gona a birnin Dakar na kasar Senegal a jiya Alhamis, wanda kwamitin nazarin cigaban tattalin arziki da al'umma na Afirka, da ofishin jakadanci na kasar Sin dake kasar Senegal suka shirya.

Yayin bude taron masana da dama daga kasashen Afirka dake halartar taron sun yi kira ga kasashen nahiyar da su dora muhimmanci kan bunkasuwar aikin gona, tare da koyi daga yadda kasar Sin ta cimma nasarar raya aikin gona a zamanance.

Sakataren kwamitin nazarin cigaban tattalin arziki da al'umma na Afirka Ebrima Sally, ya ce a halin yanzu, Afirka tana koma baya a fannin noma, kuma game da ayyukan nazarin huldar hadin kai a fannin aikin gona tsakanin Sin da Afirka, yawancinsu masanan da ba na kasashen Afirka ba ne suka kula da su.

Sally ya kuma yi kira ga masanan Afirka da su kara kokari a bangaren nazari, domin taimakawa kasashen nahiyar wajen zamanantar da aikin gona ta hanyar koyon fasahohin da kasar Sin ta samu a fannin.

A nasa bangare zaunannen wakilin hukumar abinci da aikin gona a MDD dake kasar Senegal Vincent Martin, kira ya yi ga kasashen Afirka, da su dora muhimmanci sosai kan aikin gona, ta yadda za su iya raya noma a zamanance, bisa bincike kan kimiyya da fasaha kamar yadda kasar Sin ke yi.

Shi kuwa jakadan kasar Sin a kasar Senegal Xia Huang, cewa ya yi aikin gona muhimmin fanni ne na hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka, kuma karfafa hadin gwiwar sassan biyu a wannan fanni, zai taimakawa kasashen Afrika wajen biyan bukatunsu na samar da isasshen abinci.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China