Wani sabon rahoto na MDD ya ce, yankin yammacin Afirka na da kyakkyawar damar cin moriya daga harkokin noma, muddin dai kasashen yankin suka dunkule waje guda, musamman a wannan gaba da biranensa ke dada fadada, ake kuma samun karuwar masu matsakaicin samu, da karuwar bukatu na abinci.
Rahoton wanda MDD, da bankin raya Afirka na AfDB, tare da kungiyar ECOWAS suka yi hadin gwiwar fitarwa a jiya Alhamis, wanda kuma hukumar abinci da ayyukan gona ta MDD ko FAO ta wallafa, ya kara da cewa, lokaci ya yi, da wannan yanki zai dauki matakan dunkulewa, musamman a wannan gaba da yawan al'ummarsa ya kai ga mutane miliyan 300, adadin da kuma ake hasashen zai kai ga miliyan 490 nan da shekara ta 2030.
Daukar wannan mataki, a cewar rahoton, zai samar da karin guraben ayyukan yi masu yawa, zai kuma fadada karfin tattalin arziki, tare da bunkasa hanyoyin samar da kudaden shiga, da kuma na musaya.
A daya hannun kuma rahoton ya nuna cewa, idan har yammacin Afirka na da burin yin takara da sauran yankuna a fannin cin gajiyar noma, to ya zama wajibi a kara amfani da dabarun samun fiffiko, na amfani da iri mai nagarta, da nau'o'in takin zamani mafiya dacewa, da sauran dabarun noma na zamani, tare da bincike kan hanyoyin inganta su. (Saminu)