hukumar abinci da aikin gona ta MDD ko FAO a takaice, ta shirya wani biki na musamman mai taken "sakamakon da aka samu a fannin yaki da karancin abinci" a birnin Rome na kasar Italiya, inda aka ta gabatar da takardun shaida ga kasashen da suka yi fice wajen kawar da karancin abinci. Ya yin taron na jiya Lahadi, an baiwa kasar Sin takardar shaidar cimma kudurin taron shugabannin kasashen duniya game da samar da abinci.
Cikin jawabin da ya gabatar yayin bikin, mataimakin firaministan kasar Sin Wang Yang, ya ce gwamnatin Sin na dora muhimmancin gaske ga batun samar da abinci da aikin gona, ta na kuma dukufa wajen kyautata manufofin aikin gona, da bada kwarin gwiwa ga manoma. Ya ce Sin na samar da kayayyakin aikin gona, da kyautata yanayin aikin gonan, da kuma raya kimiyya da fasaha a fannin aikin gona da samar da na'urori masu inganci domin cimma nasarar da aka sanya gaba.
Mr. Wang ya ce ya zuwa shekarar bara, an kara yawan abincin da ake samu a kasar cikin shekaru 11 da suka gabata, inda yawan sa ya kai fiye da ton miliyan 600 ko fiye a shekaru biyu da suka gabata.
Ban da haka kuma, Mr. Wang Yang ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen waje a fannin aikin gona, da kara hafafa hadin gwiwa tare da hukumar FAO, da ma sauran kasashen duniya, za kuma ta ci gaba da ba da taimako ga sauran kasashe masu tasowa, domin cimma burin ganin an magance matsalar yunwa a daukacin sassan duniya.(Lami)