Bincike cikin hadin gwiwa kan noma na taimakawa shawarwari tsakanin masanan Sin da Afrika
Kwararrun Afrika sun shawarta bincike cikin hadin gwiwa domin rike shawarwari tsakanin masanan Afrika da na kasar Sin a yayin wani dandali mai taken "Jarin kasar Sin a cikin noma a Afrika" da ya gudana a ranakun 9 zuwa 10 ga watan Afrilu a birnin Dakar. A cewar sakataren zartaswa na kwamitin kula da ci gaban bincike kan zamantakewar al'umma a Afrika (CODESRIA), Ebrima Sall, irin wadannan bincike za su kasancewa wani matakin farko kan dangantaka tsakanin Sin da Afrika a fannin noma, da kuma kan bullo da shirye shirye har zuwa ga tsara bincike da fitar da sakamako.
Mista Sall ya nuna cewa akwai wata masana'antar bincike ta Afrika dake bunkasuwa a kasar Sin, haka kuma akwai wata masana'antar bincike ta kasar Sin dake samun bunkasuwa a Afrika ko da yake wadannan bincike har yanzu ba su cimma wani matsayi ba a Nahiyar. Hukumomin binciken Afrika ba su da kwarewa sosai, kana kuma akwai hauhawar farashi a fannin bincike a yayin da kudaden da ake kebewa a wannan bangare suka ragu, in ji a nasa bangare dokta Philip O Ojo na kwamitin kasa kan irin noma na kasar Najeriya. (Maman Ada)