Cibiyar musayar sadarwa mai fadin muraba'in mita 600, da motocin sufuri masu dauke da na'urar GPS 50 na aiki yadda ya kamata, a yankin sufuri na kamfanin sayar da kayayyakin noma na Luzhuo dake lardin Shanxi na nan kasar Sin. Hakan wata fasahar zamani ce wadda hukumar kasuwanci ta kasar Sin ta samar domin baiwa kamfani damar zama abin koyi, a fannin sufurin kayayyakin noma ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo.
Irin wannan fasaha na yaduwa sosai a yanzu haka, bisa kara sauri da gwamnatin kasar Sin ta yi a fannin fitar da sabbin hanyoyin bunkasa tattalin arziki. Hakan ya sa muhimman fannoni uku wato na sha'anin noma, da raya kauyuka da manoma, na dada bunkasa ta hanyar amfana daga fasahar yanar gizo, suna kuma kara tasiri ga masu sayayya.
Wata shawara game da yadda za a bunkasa ayyukan ciniki ta yanar gizo, da kara saurin bunkasuwar tattalin arziki wadda majalisar gudanarwa ta bayar a karshen watan Mayun wannan shekara, ta nuna bukatar bunkasa ayyukan ciniki ta yanar gizo da aikin sufuri tare, kuma ta tabbatar da wasu matakai da za a dauka.
Hada fasahar yanar gizo da wadannan manyan ayyuka uku ya zama sabon salo na bunkasa sha'anin noma, irin wannan salo baya ga taimakawa saye da sayarwa ta yanar gizo, a daya hannun wasu masana na ganin burin da Sin za ta cimma shi ne hada fasahar yanar gizo da wadannan ayyuka uku tare domin samun karin moriya ta fuskar sha'anin noma, ta yadda za a ba da tabbaci ga ingancin abinci, da ba da taimako wajen warware wasu matsaloli da a kan fuskanta a wannan fanni, ciki hadda wahalar sayar da kayayyaki saboda rashin isasshen bayanai kan kayayyakin noma. (Amina)