Bankin jama'ar kasar Sin ya sanar a daren jiya Lahadi cewa, an rage kudin ruwa na rance kashi 0.25 cikin dari zuwa kashi 5.1 cikin dari. Kana yawan kudin ruwa na kudin da aka saka cikin banki ya ragu da kashi 0.25 cikin dari wato wanda zai kai kashi 2.25 cikin dari tun daga yau 11 ga wata.
Matakin rage kudin ruwa da babban bankin kasar Sin ya dauka bai wuce abin da aka iya tsammani ba, a cikin makonni biyu da suka gabata, kasuwar hada-hadar kudi na yi hasashe kan wannan batu, musamman ma a yayin da ba a samu bunkasuwar tattalin arziki mai kyau ba a watan Afrilu.
An samu sakamako wajen yin bincike kan manufar babban bankin kasar Sin cewa, bankin na fatan za a cimma burin samun bunkasuwar tattalin arziki a kai a kai. Bankin ya kara da cewa, an rage kudin ruwa sabo da yin amfani da rawar da kudin ruwa ke takawa kan tattalin arziki, ta yadda za a rage kudin da za a kashe wajen tattara kudade domin raya tattalin arziki yadda ya kamata.(Lami)