in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin kasar Sin na bunkasa kamar yadda ake fata
2015-05-01 16:15:59 cri
Manyan shugabannin kasar Sin sun jaddada cewa, bunkasar tattalin arzikin kasar a cikin watanni uku na farkon wannan shekara na tafiya kamar yadda ake zato duk da matsalin lambar da ake fuskanta.

Wata sanarwar da aka fitar bayan taron hukumar kula da harkokin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS wanda babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS Xi Jinping ya shugabanta ta bayyana cewa, kamata ya yi a mayar da hankali kan wannan matsalin lamba, bullo da matakan da suka dace a dauka, bullo da manufofi da daukar matakai a kan lokaci don tabbatar da dorewar wannan bunkasuwa.

Bugu da kari, taron ya yi alkawarin ganin ci gaban manufofin da suka shafi tattalin arzikin cikin gida da hanzarta aiwatar da gyare-gyare da bude kofa don samun ci gaba mai dorewa.

Daga karshe taron ya bayyana cewa, har yanzu guraben ayyukan yi a cikin watanni uku na farkon shekara na nan kamar yadda ake fata kana kudaden shiga da magidanta ke samu na ci gaba da karuwa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China