Ya ce, yayin da ake cin karo da tangal-tangal a bangaren tattalin arzikin Sin, kasar na da manufofin kudi da dama da za ta dauka, don tabbatar da karuwar tattalin arziki, da yawansa ya kai sama da kashi 6 cikin 100.
Kevin Rudd ya kara da cewa, yanzu haka Sin na kara kwarjininta ta hanyar yin hadin gwiwar tattalin arziki da ragowar kasashen duniya, kuma shirin ziri daya hanya daya, da tunanin game da bankin AIIB, za su taimakawa kasar zama wata babbar abokiyar zuba jari ga sauran kasashen duniya, kuma kudinta na RMB zai kara yin tasiri a duniya. Kaza lika kasar ta Sin ba ta da aniyar haifar da kalubale ga tsarin duniya, ko doka da oda, abun da take fata bai wuce gudanar da garambawul ba. (Bako)