Mr. Ban ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da kwamishina mai lura da harkokin wanzar da zaman lafiya da tsaro na kungiyar AU Smail Chergui wanda ya gudanar da ziyarar aiki a birnin New York.
Jami'an biyu sun tattauna batutuwa da suka shafi bangarorin hadin gwiwa tsakanin MDD da AU, musamman batutuwan da suka jibanci tashe-tashen hankula da ayyukan ta'addanci dake addabar wasu yankunan Afirka, kamar yankunan manyan tafkuna, da Arewacin Mali da kuma Sudan ta Kudu. Sai kuma batun kammala nazarin ayyukan wanzar da zaman lafiya wanda babban kwamitin MDD ke gudanarwa.
A karshen tattaunawar, sassan biyu sun bayyana gamsuwa da irin nasarar da ake samu, karkashin hadin gwiwa tsakanin MDD da kungiyar AU, tare da fatan dorewar hakan a nan gaba. (Saminu Alhassan)