Kakakin Ban Ki-moon Stephane Dujarric ya bayyana haka ne a wannan rana yayin taron maneman labaran da aka saba yi a hedkwatar MDD dake birnin New York.
Mr.Dujarric ya bayyana cewa, yayin ganawa da dama da Ban Ki-moon ya yi da wasu shugabannin yankin, ciki hada da shugabannin kasar Japan, Mr.Ban ya sha bayyana fatan cewa, za a samu fahimtar juna yadda ya kamata tsakanin bangarorin da abin ya shafa, ta yadda za a shimfida makoma mai kyau bisa hadin gwiwa da kuma amincewa da yadda aka taba aikata laifuffuka a tarihi.
Bugu da kari, Ban Ki-moon yana fatan cewa, bikin tunawa da cikon shekaru 70 da kawo karshen yakin duniya na biyu zai kasance wata damar da za ta iya sa kaimi ga dukkanin kasashen da abin ya shafa su koyi darussan tarihi da kuma neman ci gaba cikin hadin gwiwa a nan gaba.
A ranar Juma'a mai zuwa ne ake sa ran firaministan kasar Japan Abe Shinzo zai yi jawabi mai taken "Maganar Shinzo", wadda za ta kasance kudurin da majalisar ministocin kasar ta tsara.
A shekarar 1995, watau bayan shekaru 50 da kasar Japan din ta yi sallama da yakin duniya na biyu, firaministan kasar Japan na wancan lokacin, Tomiichi Murayama ya gabatar da jawabin Murayama, inda ya ambaci laifuffukan da kasar Japan ta aikata wadanda suka kai ga tayar da yakin duniya, ya kuma roki gafara dangane da yakin da kasar ta tayar da kuma irin ta'asa da mulkin mallakar da ta yi a ketare, daga bisani kuma, kowa ce gwamnatin kasar Japan da ta zo ta kan dora kan wannan jawabi na Murayama. (Maryam)