A jawabin da ya gabatar yayin bikin Ban Ki-moon ya bayyana cewa, kasashe membobin MDD sun cimma daidaito kan ajendar samun bunkasuwa mai dorewa bayan shekarar 2015 a kwanakin baya, kuma matasan kasa da kasa sun ba da gudummawa wajen samun nasarar wannan ajendar, kana ya kamata matasa su halarci taron ajendar don cimma burin samun bunkasuwa mai dorewa.
Hakazalika kuma, Ban Ki-moon ya ce, kamata ya yi matasa su fuskanci kalubalen talauci, rikice-rikice, rashin aikin yi da dai sauransu, kana su zama masu bada jagoranci wajen aiwarar da ajendar. Ya kamata kuma matasan kasa da kasa su yi hadin gwiwa tare da MDD don sa kaimi ga cimma burin samun kyakkyawar makoma. (Zainab)