Mista Ban Ki-moon ya fadi haka ne a lokacin da yake mayar da martini ga shakkar da kasar Japan ta yi masa game da kudurinsa na halartar bukukuwan faretin soja da kasar Sin za ta shirya a nan Beijing a ran 3 ga watan Satumba mai zuwa.
Mista Ban Ki-moon ya kara da cewa, ziyarar da zai kawo wa kasar Sin ziyara ce a karo na 9 a cikin shekaru 9 da suka gabata bayan da ya hau kan mukamin babban sakataren MDD. Ya ce zai halarci bukukuwan tunawa da ranar cika shekaru 70 da kawo karshen yakin kin harin sojojin Japan da za a shirya a nan Beijing, ya bayyana fatar cewa, yana jiran ganawar da zai sake yi da shugaba Xi Jinping, sannan kuma zai mika wa kasar Sin godiya domin gudummawar da ta ke ba MDD.
Game da shakkar da bangaren Japan ya yi masa, Mr. Ban Ki-moon ya yi bayanin cewa, "a kusan duk duniya ana bukukuwan murnar cika shekaru 70 da kawo karshen yakin duniya na biyu, wato basira ce mafi tsanani a cikin tarihin dan Adam, ana kuma murnar cika shekaru 70 da kafuwar MDD. A lokacin da ake waiwayen tarihi, za'a iya ganin irin darasin da ya kamata dan Adam ya koya, wannan yana da muhimmanci. A waje daya kuma, za a iya yin kokarin neman wata kyakkyawar makoma mai haske bisa darussan da aka koya daga tarihi." Wannan in ji shi dalili ne ya sa ya karbi gayyatar da shugaba Xi Jinping ya yi mishi zuwa kasar Sin.
A ran Jumma'a 28 ga wata, ma'aikatar harkokin wajen kasar Japan ta ce, kudurin da Ban Ki-moon ya tsaida na halartar bukukuwan murnar cika shekaru 70 da samun nasarar kawo karshen harin sojojin Japan da kasar Sin za ta shirya, kuduri ne da ya kamata a yi taka tsantsan, sannan ta nemi Ban Ki-moon da ya tsaya kan matsayin 'yan ba ruwanmu. (Sanusi Chen)