Bisa labarin da aka samu, an ce, an harba harsasan roka da dama a arewacin kasar Isra'ila dake yankin iyakar dake tsakanin kasar da kasar Syria a ranar Alhamis 20 ga wata, a ranar Jumma'a 21 ga wata kuma, sojojin saman kasar Isra'ila sun keta iyakar tsagaita bude wuta, inda suka kai harin boma-bomai na sama a kasar Syria.
Dangane haka, nan da nan rundunar sojan sa ido da MDD ta aike zuwa yankin iyakar kasar Syria tare da yin kira da rundunar sojan kiyaye kasa ta Isra'ila da rundunar sojan kasar Syria, domin sassauta yanayin da ake ciki a halin yanzu, ya zuwa yanzu, ba a samu labarin karin hare-hare a yankin ba.
A cikin sanarwar, Ban Ki-moon ya bukaci bangarorin biyu da kada su lalata aikin shimfida zaman lafiya da zaman karko da aka aiwatar a yankin a halin yanzu, tare da yin kira da su kai zuciya nesa, don gudun bata yanayin a yankin. (Maryam)