in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Magatakardar MDD ya jaddada rashin amincewa da duk wani nau'in ha'inci daga ma'aikatan kiyaye zaman lafiya
2015-08-14 09:57:08 cri
Sakamakon zargin cin zarafi a kan ma'aikatan kiyaye zaman lafiya a jamhuriyar Afrika ta tsakiya, Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon a ranar alhamis din nan yace za'a aiwatar da dokar hana duk wani nau'i na ha'inci akan kowane ma'aikaci.

Ban Ki-Moon ya fadi haka a wani taro na bidiyo da zummar tattaunawa cikin gaggawa da shugabannin ayyukan kiyaye zaman lafiya da kwamandodjin rundunar sojin su da kwamishinonin 'yan sanda akan batun binciken cigaba da cin zarafin mata da tozarta jama'a da ma'aikatan ke yi da kuma sauran ayyukan ha'inci.

Kakakin magatakardar Stephane Dujarric ya shaida ma manema labarai cewa shugaban ayyukan kiyaye zaman lafiya a jamhuriyar Afrika ta tsakiya Babacar Gaye dan asalin kasar Senegal ya ajiye aikin shi sakamakon rahoton da hukumar kare hakkin bil adama na Amnesty ta fitar akan zargin wani ma'aikacin kiyaye zaman lafiya ya harbe wani mutum da dan sa har lahira sannan yayi ma diyar mutumin 'yar shekaru 12 fyade a kasar.

Kamar yadda Ban Ki-Moon ya tabbatar a ranar laraban wannan makon ya kuma jaddada cewa rundunar tsaro da 'yan sanda daga kasashen da suka bada nasu gudunmuwa nauyi ya rataya a wuyan su a tabbatar da cewa ma'aikatan da suka tura aikin suna da cikakken horo na sanin makaman aikin su yadda doka ya tanada da kuma da'ar aiki don haka idan aka samu kowane ma'aikaci da laifin gudanar da akasin haka zasu fuskanci hukunci yadda yake a doka kuma majalissar zata bayyana hakan a cikin jerin irin wadannan laifuka.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China