in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za'a kira sabon taro kan tattaunawar siyasar kasar Libya a mako mai zuwa a Geneva
2015-08-29 13:29:44 cri
Za'a kira wani sabon zagaye na tattaunawar siyasa game da kasar Libya a birnin Geneva a tsakanin ranakun 3 da 4 na wata mai kamawa, in ji ofishin ayyukan nuna goyon bayan kasar ta Libya na MDD.

A cikin sanarwar da ta fitar ranar Jumma'a ta ce sakamakon kammala taro na kwanaki biyu a birnin Skhirat na Morroco, ofishin nuna goyon baya na MDD ta yi nuni da cewa za'a kira wani sabon zagayen tattaunawar a ofishin majalissar dake birnin Geneva domin kammala tattaunawar da nufin ganin yarjejeniyar siyasar kasar ya kai matsayin da za'a rattaba ma hannu.

Ofishin ya bayyana tattaunawar da aka yi a Morocco da cewa an samu ci gaba kuma yana da ma'ana, yanayin da imanin da mahalartan suka nuna wajen ganin an kai ga samun matsaya ya zama abin bukata cikin sauri.

Manzon MDD Bernardino Leon ya bayyana fatan shin a cewa jam'iyyar GNC za ta sake shiga tattaunawar a Geneva bayan da ta kaurace a taron Skhirat sakamakon murabus din da mambobinta biyu suka yi tare da neman ba su lokaci su sake kimtsawa.

Ya ce ofishin ayyukan bada goyon bayan zai nace wajen tuntubar masu fada a ji a kasar ta Libya domin tabbatar da samun mahalarta da dama.

A lokacin taron na kwanaki biyu, mahalarta sun tattauna tare da Mr Leon a kan yarjejeniyar jam'iyyun siyasar kasar ta Libya wanda aka yi a watan Yuli da kuma wa'adin kammala tattaunawar siyasar. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China