in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya gana da shugaban Masar
2015-09-02 20:18:32 cri
A yau Laraba ne firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da shugaban kasar Masar Abdelfattah al Sisi a nan Beijing wanda ya zo kasar Sin domin halartar bikin cika shekaru 70 da Sinawa suka samu nasara a kan mayakan kasar Japan, kana shekaru 70 da kawo karshen yakin duniya na biyu.

A yayin ganawar tasu, Li Keqiang ya jaddada cewa, kasar Sin na son karfafa fahimtar juna dake tsakanin kasar Sin da kasar Masar kan harkokin siyasa, da kuma habaka hadin gwiwar kasashen biyu kan harkokin tattalin arziki da kuma harkokin kasa da kasa da shiyya-shiyya. Haka kuma yana fatan kara inganta mu'amalar dake tsakanin al'ummonin kasashen biyu ta yadda za a ciyar da dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare dake tsakanin kasashen biyu gaba da kuma inganta bunkasuwa da zaman lafiya a yankin.

A nasa jawabin, shugaba Sisi ya ce, kasarsa na gode wa kasar Sin matuka bisa ga goyon bayan da ta ke baiwa kasar Masar, kuma kasar na son ciyar da hadin gwiwar kasashen biyu a fannonin makamashi,tattalin arziki da cinikayya gaba, a kokarin janyo hankulan kamfanonin kasar Sin da su zuba jari wajen gina sabon yankin musamman da aka kebe don samar da ci gaba a mashigin ruwan Suez da ke kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China