in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin ba da lambobin yabo gabanin bikin cika shekaru 70 da Sinawa suka samu nasara a kan mayakan kasar Japan
2015-09-02 20:14:47 cri

A yau da safe ne, aka yi bikin ba da lambobin yabo ga wadanda suka ba da gudummawa a yaki da mayakan Japan, gabanin bikin cika shekaru 70 da Sinawa suka samu nasara a kan mayakan kasar Japan, bikin da ya gudana a babban dakin taron jama'ar kasa ta Sin dake birnin Beijing.

Babban sakataren kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta Sin, shugaban kasa, kana babban kwamandan askawar kasar Xi Jinping ne ya ba da lambobin yabon ga mutane guda 30 da suka hada da tsoffin sojoji ko iyalan sojojin da suka kwanta dama da manyan hafsoshi, da kawayen kasar Sin na ketare wadanda suka shiga yakin kin harin Japan inda kuma ya gabatar da wani muhimmin jawabi.

A cikin jawabin da ya bayar, shugaba Xi ya jaddada cewa, akwai bukatar samun jarumai da kuma ruhi irin jarumai domin cimma burinmmu, ya kamata a tuna da wadanda suka ba da babbar gudummawa ga kasarmu da kuma jama'ar kasarmu, sannan ya kamata a girmama jarumai, da kiyaye irin gudummawar da suka bayar, a kuma yi koyi da su kana a kula da su yadda ya kamata.

Haka kuma, ya kamata mu hada kai wajen cimma burimmu na "shekaru 100 guda biyu", watau gina wata zaman takewar al'umma mai hannu da shuni a yayin da aka cika shekaru 100 da kafa jam'iyyar kwaminis ta Sin a shekarar 2021 da kuma gina wata kasar gurguza ta zamani mai samun bunkasuwar tattalin arziki, bisa tsarin dimokuradiyya, mai wayewar kai da kuma samun daidaito a yayin da aka cika shekaru 100 da kafuwar Jamuhuriyar Jama'ar kasa ta Sin a shekarar 2049 da kuma cimma burin kasar na mai bunkasuwa da wadata baki daya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China