Ran 15 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana ra'ayin kasar Sin kan rikicin zubar da jini da ya faru a kasar Masar ran 14 ga wata yayin da ke yin hira tare da takwaran aikinsa na kasar Jordan Zhu Da ta wayar tarho.
Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ta mai da hankali sosai kan yanayin siyasa na kasar Masar, kuma ya nuna damuwa sosai dangane da yanayin kasar Masar a halin yanzu. Shi ya sa, kasar Sin ta yi kira ga bangarorin daban daban da abin ya shafa na kasar Masar da su yi hakuri don kawar da karin mutuwa ko raunukar mutane a kasar, da kuma yin shawarwari a tsakaninsu ta yadda za a tabbatar da kasancewar doka da oda da zaman dorewa ga al'ummar kasar. Ya kuma nuna imani cewa, babu shakka kasar Masar za ta iya warware matsaloli da kalubalolin da ke gaban su a halin yanzu ta yadda za ta iya cimma burin shimfida zaman karko da ci gaban kasa. (Maryam)