in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da wakilai daban-daban daga yankin Taiwan
2015-09-01 14:22:47 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da wakilai daban-daban, ciki hadda Mista Lian Zhan daga yankin Taiwa.

Jami'an sun gana ne da shugaba Xi a Talatar nan a birnin Beijing, yayin da suka iso Beijing domin halartar bukukuwan tunawa da cika shekaru 70 da samun nasarar yakin kin harin Japan, da yaki da masu ra'ayin fin karfi.

Yayin tattaunawar tasu, shugaba Xi ya jaddada cewa nasarar da Sinawa suka samu a yakin kin harin Japan, ta kasance cikakkiya ta fuskar tinkarar hari daga kasashen waje, tun cikin tsakiyar karni na 19, wanda kuma ya dogara bisa ga hadin gwiwar da jama'ar babban yankin Taiwan suka bayar.

Ya ce ya kamata jama'ar su kula da wannan tarihi, tare da tunawa da jarumai da suka sadaukar da rayukansu yayin yakin, da kara hadin gwiwa tsakaninsu don kiyaye sakamakon da aka samu. Kaza lika ya kamata su hada kansu don ciyar da dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu gaba, a kokarin cimma burin farfadowar al'ummar kasar Sin. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China