in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya bukaci fadada dangantaka da Masar
2014-08-04 11:09:17 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana bukatar fadada dangantaka dake tsakanin kasar Sin da Masar, ta yadda hakan zai baiwa bangarorin biyu karin damar cin moriyar dangantakarsu.

Mr. Wang wanda ke ziyarar aiki ta yini biyu a kasar ta Masar, ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da takwaransa na Masar Sameh Shukry.

A nasa jawabi Mr. Shukry ya ce Masar na da burin bunkasa hadin gwiwa da Sin, a hannu guda kuma tana fatan shigar masu zuba jari daga bangaren kasar ta Sin, musamman a fannonin gina ababen more rayuwa, da makamashi, da fannin bunkasa noma da kere-kere. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China