in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron tunawa da cika shekaru 70 da samun nasarar yaki da ra'ayin fin karfi a Senegal
2015-09-02 10:57:07 cri
Masanan Sin da na kasashen Afirka sun gudanar da wani taron kara wa juna sani a birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal a jiya Talata, game da bikin cika shekaru 70 da samun nasarar yaki da ra'ayin fin karfi.

Kwamitin nazarin ilimin al'umma da bunkasuwar Afrika ne suka dauki nauyin taron, wanda kuma ya samu halartar kwararru 10, ciki hadda na jakadan kasar Sin dake Senegal Xia Huang, da wakilan gwamnatin Senegal, da shaihunnan malamai daga jami'ar Dakar.

A cikin jawabin sa, Xia Huang ya ce shekarar 2015 shekara ce ta cika shekaru 70 da samun nasarar yaki da ra'ayin fin karfi, da kuma yakin kin harin Japan, kuma Sinawa na hadin gwiwa da jama'ar duniya wajen gudanar da kasaitattun bukukuwa, domin tunawa da wannan muhimmin lokaci, da kiyaye sakamakon da aka samu, da ma kiyaye adalci a duniya, da oda da doka bisa ka'idojin tsarin mulkin MDD.

A cewar Mista Xia, Sin da Afrika suna fahimtar juna, da amincewa juna, da taimakawa juna wajen sa kaimi ga kiyaye tsarin duniya bayan yaki, da samar da wata duniya mai daidaito, da adalci, da bude kofa ga juna, da tattauna muhimman abubuwa tsakanin bangarori daban-daban. Ban da haka kuma, a karkashin taimakon 'yan uwa daga kasashen Afrika, Sin ta farfado da mukamin ta cikin MDD.

A sa'i daya kuma, Sin ta kan kiyaye moriyar Afrika bisa tsarin mulkin MDD, da kokarin jawo hankalin kasashen duniya wajen samar da taimako kan bunkasa Afrika. Ya ce Sin za ta gudanar da hadin gwiwa da kasashen duniya ciki hadda kasashen Afrika, wajen sa kaimi ga kafa tsarin kiyaye doka da oda, da tsarin duniya yadda ya kamata. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China