A yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ba da lambobin tunawa da ranar cika shekaru 70 da cimma nasarar yakin kin harin Japan ga wasu tsoffin sojoji, da hafsan-hafsoshi, da kuma kawayen kasar Sin na ketare, wadanda suka shiga yakin kin harin Japan da kuma iyalansu. Shugaba Xi ya kuma gabatar da jawabi a yayin wannan biki da ya gudana a babban dakin taron jama'ar kasar Sin. (Lami)