A lokacin ne kuma, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gabatar da wani jawabi mai muhimmanci, kana ya kalli faretin rundunonin sojan kasar.
Haka kuma, a wannan rana, Gidan Rediyon CNR, Gidan Talabijin na kasar Sin CCTV da kuma Gidan Rediyon CRI za su watsa abubuwan da ke faruwa a kan bikin kai tsaye ga duniya. Hakazakila shafin intanet na Renmin, Xinhua da kuma Gidan talebijin ta intanet na kasar Sin da kuma shafin intanet na kasar Sin su ma za su watsa dukkan abubuwan da ke wakana a dandalin kai tsaye. (Maryam)