in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon shugaban kasar Masar ya gana da manzon musamman na shugaban kasar Sin
2014-06-09 09:56:32 cri

Sabon shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi ya gana da Miao Wei, ministan masana'antu da sadarwa na kasar Sin a jiya Lahadi a birnin Alkahira, fadar gwamnatin kasar ta Masar.

Miao Wei wanda ke kasar ta Masar domin halartar bikin rantsuwar kama aiki ta shugaba Sisi a matsayin manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon taya murnar shugaba Xi ga shugaba Sisi, tare da kyakkyawan fatan cimma nasara, inda ya ce, a halin da ake ciki, kasar Sin na da burin kara cudanya ta hanyoyi daban daban da kasar Masar, tare da inganta hadin kansu don cimma moriyar juna, baya ga batun kara tuntubar juna a kan lamuran duniya da na shiyya-shiyya.

An dai yin imanin cewa, dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Masar za ta samu kyakkyawar makoma, bisa matukar kulawa da kokarin da shugabannin kasashen biyu ke yi.

A nasa bangare, shugaba Sisi ya godewa takwaransa na Sin bisa aikewa da manzon musamman domin halartar bikin rantsuwarsa ta kama aiki. Ya na mai jaddada cewa, kasashen Masar da Sin kasashe ne masu dogon tarihi, akwai kuma dankon zumunci mai karfi tsakaninsu. Ya ce yanzu haka kasar Masar na cikin wani lokaci mai wuya, don haka take fatan kasar Sin, za ta ci gaba da ba ta tallafi da goyon baya a fannoni daban daban. Shugaba Sisi ya kara da cewa akwai sirri tsakanin kasashen biyu ta fuskar hadin kansu, kuma Masar na maraba da zuwan masana'antun kasar Sin domin zuba jari.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China