in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da aikin share gafen babban taron tunawa da cika shekaru 70 da cimma nasarar yakin kin harin Japan
2015-08-23 14:30:32 cri

Don tabbatar da babban taron tunawa da cika shekaru 70 da cimma nasarar yakin kin harin Japan kuma yaki da masu nuna ra'ayin fin karfi a duniya, an yi aikin atisayen sojoji daga daren ran 22 ga wata zuwa safiyar ran 23 ga wata a filin Tian Anmen da titin Chang Anjie.

Bisa labarin da aka bayar, sojoji daga kasashe fiye da 10 ciki hadda Rasha, Kazakhstan, Mongolia da sauransu, sun halarci fareti, wanda ya kuma samu halartar sojojin kasar Sin fiye da dubu 10, na'urorin sojin kasar sama da 500, jiragen sama kimanin 200. Ban da wannan kuma, rukunin kiyaye tutar kasa, kungiyar 'yan badujala, kungiyar 'yan amshin murya, rukunin harba igwar taya murna su ma sun halarci faretin. Dadin dadawa, jama'a kimanin dubu 35 sun samu damar kallon wannan biki. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China