in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wurare daban-daban na kasar Sin sun gudanar da bukukuwan tunawa da cika shekaru 70 da samun nasarar yakin kin harin Japan
2015-09-01 11:10:32 cri

A 'yan kwanakin nan, wurare daban-daban na kasar Sin sun gudanar da bukukuwan tunawa da cika shekaru 70 da samun nasarar yakin kin harin Japan.

An bude dakin nuna kayayyakin tarihi na yakin kin harin Japan, wanda Sin da Amurka suka yi hadin gwiwar gudanarwa, a ran 31 ga watan Agusta a birnin Guilin na lardin Guangxi. Wannan daki ya kuma nuna wasu kayayyakin da rundunar sojin sa kai ta kasar Amurka dake kasar Sin ta yi amfani da su a waccan lokaci, ciki hadda buraguzan jiragen saman rundunar, da kayayyakin sojojin saman Amurka da suka rasu bayan da jiragen samansu suka gamu da hadurra.

Ban da wannan kuma, an kaddamar da bikin kai ziyara wasu wurare dake da nasaba da wannan yaki a wannan rana, a dakin adana abubuwan dake shaida laifuffukan da rundunar sojan Japan mai lamba 731 ta yi a birnin Heilongjiang.

Dadin dadawa, an sake gano wasu littattafai dangane da labaran kasar Sin a yankin arewa maso gabashin kasar Sin, wadanda jami'ar Nankai ta buga kafin barkewar wannan yaki, littattafan da suka ilmantar da daliban jami'a, da makarantun midil, da na 'yan mata da firamare a waccan lokaci. Don tunawa da cika shekaru 70 da samun nasarar yakin kin hari Japan, da ra'ayin fin karfi, jami'ar Nankai da kungiyar nazarin tunanin tsohon shugaban jami'ar Zhang Boling, sun yi shirin sake gyarawa tare da buga wadannan littattafai,. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China