A jawabinsa wani wakili ya ce, yakin da kasashen Fascist da suka hada da Jamus da Japan da sauransu suka tayar a shekaru sama da 70 daga bana, ya yi mummunar illa ga al'ummar duniya, wannan ya sa aka kira wannan taro domin jama'a su tuna da wadannan abubuwan da suka faru a tarihi.
Haka kuma, jakadan kasar Sin dake kasar Jamus ya bayyana cewa, cikin shekaru 70 da suka gabata, bayan da aka kawo karshen yakin duniya na biyu, kasar Jamus ta dukufa wajen tunana laifuffuka da ta aikata a yayin yakin da kuma tsayawa tsayin daka wajen kiyaye zaman lafiya, lamarin da ya sa, kasar ta Jamus sake samun amincewa da mutunci daga kasashen Turai. A sa'i daya kuma, kasar Sin na fatan kasar Japan za ta yi koyi da kasar Jamus, ta bincike laifuffukan da ta aikata wa kasar Sin da sauran kasashen Asiya yadda ya kamata, kana, ya kamata kasar Japan ta dauki matakan da suka dace na kiyaye tsarin duniya bayan yaki, da kuma neman hanyar tabbatar da zaman lafiya. (Maryam)