in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tabbatar da gano bangaren jirgin saman MH370 da ya bace
2015-08-06 10:40:25 cri

Firaministan kasar Malaysia Najib Tun Razak, ya ce bayan gudanar da bincike kan tarkacen jirgin saman da aka gano a tsibirin l'île de la Reunion dake kasar Faransa, an tabbatar da cewa sassan da aka gano bangarori ne na jirgin saman kamfanin Malaysia nan mai lamba MH370 da ya bace.

Yayin wani taron manema labaru da aka shirya da sanyin safiyar yau, Najib ya ce bayan bacewar jirgin saman dauke da fasinjoji har tsawon kwanaki 515, yana cike da alhinin bayyana cewa rukunin masu bincike ya tabbatar da cewa, bangarorin jirgin saman da aka gano a tsibirin kasar Faransa, sassa ne na jirgin saman kasar sa mai lambar MH370 da ya bace.

Najib ya ce, gwamnatin kasar za ta cika alkawarin da ta dauka na fayyace gaskiyar lamari game da wannan hadari.

A daya bangaren kuma, yayin wani taron manema labaru da ya gudana a birnin Paris, rabin sa'a bayan bayanin mahukuntan Maleshiyan, mataimakin jami'i mai gabatar da kara na kasar Faransa Serge Mackowiak, ya ce akwai babbar yiwuwar wadannan sassan jirgin da aka gano a tsibirin kasar a ranar 29 ga watan Yuli, ragowa ne na jirgin kamfanin Malaysia da ya bace.

Sai dai ya ce za a ci gaba da gudanar da bincike, inda daga Alhamis din nan kwararru za su gaggauta kammala aikin binciken da ake gudanarwa, domin gani karin shaidun da za su gamsar. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China