in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta yi jawabi game da tabbatar da samun tarkacen jirgin saman MH370
2015-08-06 13:20:31 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta yi jawabi game da tabbatar da samun tarkacen jirgin saman nan mai lamba MH370 a Alhamis din nan, inda ta ce gwamnatin kasar Sin ta nuna alhinin rashin dukkan mutanen dake cikin jirgin saman, ciki hadda fasinjojin Sin, tare da jajantawa iyalansu.

Madam Hua ta bayyana cewa, Sin ta bukaci kasar Malaysia da ta cika alkawarinta, na ci gaba da gudanar da bincike game da dalilin da ya sabbaba faruwar hadarin, da daukar matakai bayan faruwar hakan, da tabbatar da moriyar iyalan fasinjojin dake cikin jirgin saman. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China