in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Minsitan sufurin Malasiya ya tabbatar da cewa tarkacen jirgin da aka gano ya fito daga jirgin Boeing 777
2015-08-02 18:36:04 cri
Ministan sufurin kasar Malasiya Liow Tiong Lai ya tabbatar a ranar Lahadi cewa binciken da aka gudanar kan karfen jirgin saman da aka gano a tsibirin Reunion na kasar Faransa ya nuna cewa ya fito jirgin Boeing 777 da ya yi hadari watan Maris na shekarar 2014.

Ministan sufurin ya bayyana cewa hukumomin kasar Faransa sun gudanar da aikin tattancewa tare da hadin gwiwar kamfanin kera jiragen saman Boeing na kasar Amurka, hukumar da ke kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Amurka (NTSB) da kuma tawagar reshen harkokin zirga zirgar jiragen saman jama'an Malasiya, kamfanin Malasiya Airline da kwamitin ICAO dake bincike kan hadarin jirgin saman MH370. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China