Sin na maraba da maneman labaran gida da ketare a yayin bikin murnar cika shekaru 70 da nasarar yakin Fascist
A yau ne wakilin tawagar shugabannin kula da ayyukan watsa labarai na bukukuwan murnar cikon shekaru 70 da nasarar da kasar Sin ta samu wajen yakar sojojin Japan, da kuma nasarar yakin Fascist na duniya ya sanar da cewa, domin murnar cika shekaru 70 da nasarar kawo karshen yakin duniya na biyu, za a gudanar da manyan bukukuwa da dama a birnin Beijing a ranar 2 da 3 ga watan Satumba na shekarar bana, kuma ana maraba da zuwan manema labarai na gida da na waje su zo kasar Sin da su yada labarun wadannan bukukuwan da za a yi.
Haka kuma, ana bukatar manema labarai na ketare dake son halartar bukukuwan da su yi rajista a shafin intanet na reg.kzjn70.cn tun ranar 3 zuwa 18 ga watan.
Rahotanni na nuna cewa, za a kafa wata cibiyar watsa labarai a birnin Beijing a yayin da ake gudanar da wadannan bukukuwa, domin taimaka wa manema labaran ketare kan harkokin labarai. (Maryam)