in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana son yin afuwa ga wasu firsinoni sakamakon cika shekaru 70 da samun nasarar yakin kin harin Japan
2015-08-24 19:34:41 cri

A wajen taro karo na 16 na zaunannen kwamitin majalissar wakilan jama'ar kasar Sin zagaye na 12, wanda ya gudana a Litinin din nan, an tantance daftarin shirin yiwa wasu firsinoni afuwa. An dai gabatar da daftarin shirin ne domin murnar cika shekaru 70 da samun nasarar yakin kin harin Japan, da kuma samun nasarar yaki da ra'ayin nuna karfin tuwo.

An ce za a so a yi afuwa ga wadanda suka aikata laifuka iri hudu, wadanda aka fara tsare su a gidan kaso kafin ranar 1 ga watan Janairun wannan shekara da muke ciki, sai dai za a saki irin firsinonin da ake da tabbacin ba za su haifar da illa ga al'ummar kasa ba bayan fitowar ta su.

Daraktan kwamiti mai kula da harkokin shari'a da dokoki, na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Li Shishi, ya yi karin bayani game da rukunin wadannan daurarru nau'i hudu. Ya ce rukunin farko shi ne wadanda suka taba shiga yakin kin harin Japan, da yakin 'yantar da jama'ar kasar Sin. Na biyu kuwa, su ne wadanda suka shiga aikin kiyaye mulkin kan kasa, da cikakken yankin kasar bayan kafuwar sabuwar kasar Sin. Na uku, rukunin wadanda suke da shekaru sama da 75 a duniya kuma masu nakasa da ba su iya kula da kansu. Yayin da rukuni na hudu, shi ne wadanda shekarunsu bai kai 18 ba yayin da suka aikata laifi, aka kuma yanke musu hukuncin daurin kasa da shekaru 3, ko idan ya rage shekara daya a sake su bayan cikar wa'adin tsare su a gidan kurkuku. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China