Majalisar ministocin kasar Isra'ila ta kira wani taro na musamman a daren jiya Lahadi, inda aka cimma matsaya game da daukar mataki mai tsanani na yaki da ikidun Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi.
Wata sanarwar da aka fitar bayan taron ta nuna cewa, danyen aikin da wasu Yahudawa suka aikata a kauyen Duma na Palasdinu, ko shakka babu aiki ne na ta'addanci, wanda hakan ya sa majalisar ta yanke shawarar gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kotu, don hana aukuwar irin hakan a nan gaba.
Matakan da aka dauka sun hada da daure wadanda suka aikata laifin a gidan kurkuku bayan samun amincewar hakan daga babban mai daukaka kara.
Ban da haka kuma, sanarwar ta ce, majalisar ta ba da umurni da a sa kaimi ga majalisar dokokin wajen zartas da daftarin dokar yaki da ta'addanci, wadda za ta dace da manufar yankewa masu aikata laifi hukuncin da ya dace, ciki hadda irin wannan laifi da aka aikata a kauyen Duma.
Ban da wannan kuma, majalisar ministocin ta yanke shawarar kafa wani kwamiti karkashin jagorancin ministan tsaron kasar, don ba da shawara ta fuskar yaki da ta'addanci.
Dadin dadawa, kakakin hukumar tsaron kasar Isra'ila ta shaida cewa, ministan tsaron kasar Moshe Ya'alon, ya ba da umurni ga rundunar tsaron kasar da ta dauki mataki yadda ya kamata na yaki da Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi. (Amina)