in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan tsaron Amurka ya gana da firaministan Isra'ila
2015-07-22 11:34:53 cri
Ministan tsaron kasar Amurka Ashton Carter, ya gana da firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu a birnin Kudus a jiya Talata.

Wannan ne dai karo na farko da babban jami'in Amurka ya gana da Netanyahu, tun bayan da aka daddale yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran daga duk fannoni.

A cikin jawabin da Carter ya yi, bayan isar sa kasar Jordan a wannan rana, ya ce Netanyahu ya bayyana karara cewa, bai amince da matakan da Amurka ta dauka game da daddale yarjejeniya kan batun nukiliya kasar Iran ba, amma daga bisani Carter ya ce ko tsakanin abokai ma a kan samu bambancin ra'ayi.

Kasashe 6 da batun nukiliyar Iran ya shafa da ita kan ta Iran din sun daddale yarjejeniya daga dukkanin fannoni, game da batun nukiliyar Iran a birnin Vienna a ranar 14 ga wata, sai dai Isra'ila tana adawa da wannan mataki, wanda Netanyahu ya bayyana a matsayin yarjejeniyar da za ta zama babban kuskure cikin tarihi. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China