in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rikici ya barke a kan iyakar Isra'ila da Lebanon
2015-01-29 11:04:12 cri
Kakakin rundunar sojojin tsaron kasar Isra'ila ya ce mayakan kungiyar Hezbollah ta Lebanon sun harba wani makami mai linzami kan wata motar yaki ta sojojin Isra'ila, wadda ke sintiri a iyakar kasar da Lebanon.

Jami'in sojin na Isra'ila ya ce harin ya raunata sojojin Isra'ila da dama. A kuma wani mataki na maida martani, rundunar sojin Isra'ilan ta kaddamar da hare-hare bom kan wasu yankuna na kasar Lebanon. Daga bisani kuma kungiyar Hezbollah ta sanar da kai harin kan sojojin Isra'ila, lamarin da ya haddasa zaman dar-dar a yankunan dake kan iyakar kasashen Isra'ila da Lebanon.

A wani batun mai nasaba da wannan, kakakin rundunar MDD ta UNIFIL dake kudancin kasar Lebanon Andrea Tinanti, ya ce wani sojin tawagar UNIFIL ya rasu, a sakamakon harin bom da sojojin Isra'ila suka kaddamar a yankin iyakar kasar da kudancin Lebanon.

Kaza lika firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu ya gudanar da taron gaggawa domin tabbatar da tsaro a birnin Tel Aviv a daren jiya Laraba, inda aka tattauna kan yadda za a fuskanci matsanancin halin da yankin iyakar kasar da Lebanon ke ciki. Netanyahu ya bayyana cewa, Isra'ila za ta mayar da martani ga duk wani harin da aka kai mata.

Shi kuwa a nasa bangare firaministan kasar Lebanon Tammam Salam, Allah wadai ya yi da harin na sojojin Isra'ila.

Bugu da kari ita ma jami'ar MDD mai shiga tsakani dake kasar Lebanon Sigrid Kaag, ta fidda wata sanarwa, inda ta ce, MDD ta damu da halin da ake ciki a yankin kan iyakar kasashen biyu, kana ta kalubalanci bangarori daban daban da abin ya shafa, da su kaucewa daukar matakan da ka iya kara rura wutar rikici. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China