Wannan ne karo na farko da sojojin kasar Isra'ilan suka yi atisayen soja a kusa da zirin Gaza, tun bayan da aka kammala dauki-ba-dadi a zirin, cikin watan Agustar bara.
Kakakin sojojin kasar Isra'ilan dai bai bayyana yawan sojojin da suka shiga atisayen ba, sai dai ya ce, sojojin kasa da na sama na kasar, sun halarci atisayen sojan a wannan karo, kuma za su samu horo, da kara karfinsu na tinkarar batutuwan da watakila za su faru a kan iyakar kasar, kamar shigar dakarun Palesdinu cikin kasar ta Isra'ila cikin sirri, da yin garkuwa da sojojin Isra'ila, ko harba makaman roka ga kasar Isra'ila da dai sauransu.
Dama dai baya ma Isra'ilan ta taba yi atisayen soja na kwanaki biyu a yammacin gabar kogin Jordan a farkon watan nan, inda sojojin sama, da ma'aikatan leken asiri, da sojojin yaki, da kuma sojojin share-fage dubu 13 suka halarci atisayen. (Zainab)