A cikin sanarwar an bayyana cewa, sojojin share-fage kimamin dubu 13 za su halarci atisayen sojan.
Wani kakakin sojojin tsaron kasar ya shaida wa 'yan jarida a ranar 1 ga wata cewa, sojojin sama da ma'aikatan hukumar leken asiri da sojojin ruwa da na kasa su ma za su halarci atisayen sojan. A yayin wannan atisayen soja na kwanakin biyu, za a gudanar da ayyukan kwaikwayo game da yin garkuwa da jama'ar kasar, da samun rikici a tsakanin sojojin tsaron kasar da masu zanga-zanga na Palesdinu da dai sauransu. Sojojin kasar Isra'ila sun taba yin irin wannan atisayen soja a yammacin gabar kogin Jordan a shekarar 2012.
Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Isra'ila suka bayar, an ce, yin atisayen sojan yana da nasaba matsalar dake kasancewa a tsakanin Isra'ila da Palesdinu. Labarin ya tsamo wani bincike da sojojin kasar Isra'ila suka yi a kwanakin baya kan halin da ake ciki a kasar cewa, domin hukumar al'ummar Palesdinu tana fuskantar matsalar tattalin arziki, watakila Palesdinawa dake yammacin gabar kogin Jordan za su tada rikici ga Isra'ila a karshen watan Maris ko farkon watan Afrilu. (Zainab)