Sabuwar gwamnatin kasar ta kunshi ministoci 20, 12 daga cikinsu su daga jam'iyyar Likud, sai 3 daga jam'iyyar Jewish Home, da guda 3 daga jam'iyyar Kulanu, sai kuma guda 2 daga jam'iyyar Shas.
Kafin majalisar dokokin kasar ta jefa kuri'un amincewa da sabuwar gwamnatin kasar, firaministan kasar Netanyahu ya bayyana cewa sabuwa gwamnatin za ta yi kokarin raya tattalin arziki, da rage gibin dake tsakanin masu arziki da matalauta, da kuma neman samun zaman lafiya a tsakaninta da Palesdinu, ta hanyar diplomasiyya bisa tushen tabbatar da tsaron kasar Isra'ila.
Kaza lika ya bayyana cewa, zai ci gaba da gayyatar sauran jam'iyyun kasar shiga majalisar ministocin a nan gaba. (Zainab)