Wata sanarwa da ofishin firaministan Isra'ila ya bayar a jiya, ta bayyana cewa, bayan shawarwarin da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi da sassan da abin ya shafa, nan take aka amince da gina wadannan gidaje a yankin Beit El. Netanyahu ya yanke wannan shawara ce, bayan da sojojin Isra'ila suka rushe wasu gine-gine 2 a yankin Beit El.
Kwanan baya, daruruwan Palasdinu dake zaune a wannan yanki sun yi taho-mu-hama da 'yan sanda Isra'ila da suka zo rushe gine-gine, lamarin da ya haddasa mummunan tashin hankalin da ya yi sanadiyyar jikkatar mutane da dama.
Mazauna wurin sun yi jefi 'yan sandan da duwatsu, yayin da 'yan sanda suka yi amfani da barkonon tsohuwa da mesar ruwa don tarwatsa mutanen, kana an cafke masu ta da zaune-tsaye a kalla 60.
A ranar Laraba ne dai babban magatakardan M.D.D. Ban Ki-moon ya ba da wata sanarwa ta hannun kakakinsa, inda ya yi Allah wadai da matakin gwamnatin Isra'ila na gina sabbin matsugunan Yahudawa a yankin Beit El da ke yammacin gabar kogin Jordan.
Ya kuma bukaci gwamnatin Isra'ila da ta dakatar da duk wani abin da zai gurgunta shirin samar da zaman lafiya tsakanin Falesdinu da Isra'ila. Sanarwar ta Ban Ki-Moon ta jaddada cewa, gina matsugunan ya keta dokokin kasa da kasa, kuma nakusu ne ga shirin samar da zaman lafiya, kuma ya saba wa shirin kafa kasashen biyu da gwamnatin Isra'ila ta gabatar, don haka ya bukaci gwamnatin Isra'ila da ta hanzarta dakatar da wannan kuduri bisa la'akari da kokarin da ake na samar da zaman lafiya da matsayin karshe na yankin.(Bako)