A cewar mista Netanyahu, ' 'yan Falasdinu ba su da wata kasa ta kansu', bisa ka'idojin kasa da kasa, don haka ya kamata 'yan Falasdinu su yi shawarwari da kasar Isra'ila kai tsaye don neman cimma burinsu na kafa wata kasar kansu. Sai dai, a cewar Netanyahu, kotun duniya ta yi watsi da wannan batu, da ka'idarta cewa wata kasa kadai ke da ikon kai kara wajen kotun. Sabili da haka, shawarar da kotun ta yanke ta gudanar da bincike kan Isra'ila ba ta dace ba ko kadan.
Kafin haka kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya da ke da cibiya a birnin Hague na kasar Holland ta sanar a ranar 16 ga wata cewa, za ta yi bincike kan kasar Isra'ila don gano ko akwai alamun laiffukan yaki da bangaren Falasdinu ya zargi Isra'ila da aikatawa.(Bello Wang)