in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasa da kasa na taya kasar Sin murnar samun karbar bakuncin wasannin Olympic na shekarar 2022
2015-08-01 14:16:34 cri

Biranen Beijing da Zhang Jiakou sun cimma nasarar samun damar karbar bakuncin wasannin Olympic na shekarar 2022 a jiya Jumma'a ran 31 ga watan Yuli, abin da ya sa Beijing zama birni na farko a duniya da ya shirya wasannin Olympic na yanayin sanyi da na zafi. Dalilin haka, kasashe daban-daban sun taya Sinawa murnan wannan nasara.

Hukumar kula da wasan motsa jiki ta kasar Sin, kungiyar wasan motsa jiki ta al'ummar Sin da kwamitin mai kula da harkokin Olympic na Sin sun ce, da wannan zarafi na karbar bakuncin wasan Olympic na yanayin sanyi, Sinawa wadanda yawansa ya kai kashi 1 cikin 5 bisa na dukkanin jama'ar duniya za su kara fahimtar manufar Olympic wato hadin gwiwa, sada zumunci da samun zaman lafiya, haka kuma abin zai karawa Sinawa himma wajen shiga wasannin motsa jiki a yanayin sanyi da sauran sana'o'i dake da nasaba da shi, ban da haka kuma, zai ba da gudunmawa ga bunkasa ayyukan lafiyar Sinawa da wasannin motsa jiki na Olympic.

Dadin dadawa, a yayin da yake zantawa da manema labaru a ran 31 ga watan Yuli, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Amurka Mark Toner ya ce Amurka na taya kasar Sin murnar cimma nasarar, kuma ya ce, birnin Beijing ya cimma nasarar daukar bakuncin wasannin Olympic na yanayin zafi na shekarar 2008, saboda haka mun yi imani cewa, birnin Beijing ya cancanci daukar bakuncin wannan wasa.

Ban da haka kuma, a wannan rana, gidajen talabijin da dama, da wasu kafofin yada labaru na kasar Faransa sun taya birnin Beijing da Zhang Jiakou murna jim kadan bayan gabatar da sunan birnin Beijing a matsayin mai masaukin bakin wannan gasa.

Haka kuma, gidajen talabijin da jaridun kasar Japan su ma sun ba da labari kan lamarin, inda suka bayyana cewa, muhimmin ginshikin da ya taimaka wa Beijing samun wannan matsayi shi ne goyon baya daga gwamnati da shugabannin kasar Sin, sannan da kyakkyawan yanayin tsarin kudi da kuma cigaba da birnin Beijing ke da su.

Ko da yake, birnin Alma-Ata na kasar Kazakhstan ya kasa samun wannan dama, kafofin yada labaru daban-daban na kasar sun darajanta ayyukan da birnin Beijing ya yi, kuma sun amince da cewa, birnin Beijing zai samun nasara wajen shirya wannan gasa saboda ganin nasarar da ya samu a shekarar 2008. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China