in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na da niyyar cimma nasarar daukar bakuncin wasan Olympics na 2022
2015-07-31 17:10:52 cri
Mataimakiyar firaministan kasar Sin Liu Yandong, ta ce Sin na da kwanciyar hankali, da wadatar tattalin arziki, da kyakkyawan yanayin zamantakewar al'umma, wanda zai ba ta cikakkiyar damar karbar bakuncin gasar Olympics ta yanayin sanyi a shekarar 2022.

Madam  Liu ya bayyana hakan ne ga manema labaru, jim kadan bayan kammalar cikakken taro karo na 128, na kwamitin shirya wasannin Olympic na kasa da kasa, wanda ya gudana a birnin Kuala Lumpur, fadar mulkin kasar Malaysia.

Ta ce a matsayin ta na 'yar takara, Sin ta cimma nasarar shirya gasar Olympics a shekarar 2008, a yayin da biranen Beijing da Zhang Jiakou ke da dukkanin cancanta ta karbar bukincin gasar shekarar 2022 mai zuwa.

Kaza lika Madam Liu ta ce gwamnatin kasar Sin, za ta samar da tallafi iyakacin karfin ta a dukkan fannoni, ciki hadda batun kudi, da kare doka, da tsaro, da tsarin gudanarwa da dai sauransu. Bugu da kari Sin na da niyyar sake cimma gagarumar nasara wajen gudanar da gasar ta Olympics, kamar yadda ta samu wannan nasara a shekarar 2008.

Ta ce Sinawa na matukar goyon bayan tawagar Sin mai neman karbar bakuncin wannan gasa ta Olympics ta yanayin sanyi a shekarar 2022. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China