Sakamakon hakan, wakilan birnin da hadin gwiwar wakilan kwamitin kula da wasannin Olympic na kasa da kasa (IOC), sun kira taron manema labarai a birnin Kuala Lumpur, fadar mulkin kasar Malaysia. Inda shugaban kwamitin na IOC Thomas Bach ya taya birnin Beijing murnar samun wannan dama, tare da nuna yabo ga birnin, bisa kokarin sa na cimma wannan nasara.
A nasa bangare, magajin garin birnin Beijing Wang Anshun, ya alkawarta cewa, Beijing zai shirya wa al'ummar duniya gasar wasannin Olympic mai matukar kayatarwa. Ya kuma gayyaci al'ummar duniya da su dunguma zuwa birnin Beijing a shekarar 2022 domin halartar gasar ta Olympic.(Lubabatu)